Rahoto: Jarin kasar Sin ke taimakawa bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka
2024-08-28 09:40:07 CGTN Hausa
A kashen makon da ya gabata ne cibiyar bunkasa zuba jari a nahiyar Afirka ta kasar Sin (CABC), ta kaddamar da rahoto game da jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a nahiyar Afrika na 2024.
Rahoton wanda aka kaddamar da yammacin ranar Juma’a da ta gabata, ya bayyana nasarorin da aka samu, da sabbin bangarori, da ma damammakin zuba jari dake akwai a kasashen Afrika.
An fara fitar da rahoton ne tun daga shekarar 2021, kuma hakan bangare ne na sakamako dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika ko FOCAC, karkashin jadawalin aikin da ake son gudanarwa daga 2021 zuwa 2024, wanda aka fitar a birnin Dakar na kasar Senegal. An fitar da rahoton na karshen mako, gabanin taron FOCAC da za a gudanar a birnin Beijing nan da ‘yan kwanaki.
Mahalarta taron sun bayyana dandalin FOCAC a matsayin wata kadara mai daraja ga Sin da Afrika, suna masu ammanar cewa cikin shekaru 3 masu zuwa, karkashin dabaru daga gwamnatocin Sin da Afrika, da goyon baya daga bangarorin diplomasiyya da cinikayya da hada-hadar kudi, hadin gwiwar Sin da Afirka a bangarorin tattalin arziki da cinikayya da zuba jari, zai kai ga zamanantar da nahiyar Afirka.
Rahoton dai ya ce zuwa karshen shekarar 2022, jarin da Sin ta zuba kai tsaye a nahiyar Afrika ya zarce dala biliyan 47, kuma sama da kamfanonin Sin 3,000 ne suka zuba jari, tare da gudanar da harkokin kasuwanci a Afirka. Kana a rabin farko na shekarar 2023, jarin kai tsaye na Sin a Afrika ya zarce dala biliyan 1.82, adadin da ya karu da kaso 4.4 bisa dari a kowacce shekara.
Rahoton ya kara da cewa, kasar Sin na kara yawan jarinta a Afrika a bangarori daban daban, inda ta kara fadadawa zuwa bangarorin masu tasowa, kamar na tattalin arzikin dijital, da ayyukan sarrafa hajoji ba tare da gurbata muhalli ba, da sufurin sama, da hidimomin kudi, da cinikayya ta yanar gizo da sauransu.
Bugu da kari, rahoton ya ce ta hanyar zuba jari dake mayar da hankali ga harkokin kasuwanci, jarin Sin kan ababen more rayuwa da sauran sabbin bangarori, suna bunkasa tsarin ayyukan masana’antu da ma daukaka darajarsu.
Rahoton ya tabbatar da shirin da Sin ke da shi na kara karfafawa kamfanonin kasar gwiwar zubawa, da fadada jarinsu a kasashen Afirka, tare da kira ga gwamnatocin nahiyar Afirka da su kyautata muhallin kasuwanci, da inganta dangantakar Sin da kasashen nahiyar, wanda hakan zai haifar da karin nasarori a cudanyar sassan biyu. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Faeza Mustapha)