Sama da mutane dubu 12 ne ambaliyar ruwa ta yi sanadin rasa muhallansu a jihar Adamawa
2024-08-28 10:09:34 CMG Hausa
Yankuna 21 ne dake kananan hukumomi 3 na jihar Adamawa suka fuskanci matsalar ambaliyar ruwa wadda ta yi sanadin rasa muhallan mutane sama da dubu 12 sannan kuma wasu shidda sun rasa rayukansu.
Babbar sakatariya a hukumar bayar da gajin gaggawa ta jihar Adamawa Dr. Celine Laori ce ta tabbatar da hakan jiya Talata 27 ga wata, lokacin da take zagayawa da gwamnan jihar Amadu Fintiri wuraren da ruwan ya yi barna, ta ce yanzu haka da yawa mutanen yankunan suna samun mafaka ne a gine-ginen hukuma.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahato.
Dr. Celine ta ce, kananan hukumomin da wanann ambaliyar ruwa ta fi shafa sosai sun hada da Madagali, da Demsa da Numan, inda ta ce baya ga kawo tsaiko ga harkokin yau da kullum na al’umomin, ambaliyar ruwa ta yi sanadin karyewar gada da ta hade garuruwa da dama, da rushewar gidaje da shaguna da gine-ginen asibitoci da makarantu, sannan kuma ta mamaye gonaki.
A lokacin da yake jajanta abun da ya faru tare da gabatar da tallafin kayan abinci da na kwanciya da magunguna, gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta fara nazarin sake gina gadar da ta karye wadda ta hade garuruwa da dama.
“Yanzu ina tare da dan kwangilar da zai gudanar da aikin domin dai mu duba abun da za mu yi wajen ganin mun hade kananan hukumomi biyun da gadar ta raba, amma duba da yanayi ba aiki ba ne da za a fara shi nan da nan, a don haka muna shawartar al’ummomi da su kara nuna juriya da hakuri.” (Garba Abdullahi Bagwai)