Sakatare janar na MDD ya yi tir da harin da aka kai Burkina Faso
2024-08-28 11:01:51 CMG Hausa
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin ta’addanci da aka kai yankin tsakiyar Burkina Faso, a karshen makon da ya gabata.
Yayin taron manema labarai a jiya, kakakin sakatare janar din Stephane Dujjaric, ya ruwaito Antonio Guterres na jajantawa wadanda harin ya rutsa da su, da iyalansu da ma al’ummar Burkina Faso, inda ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki.
Mutane da dama, galibi fararen hula ne suka mutu sanadin wani harin da aka kai yankin Barsalogho na arewa maso tsakiyar kasar a ranar Asabar.
Har ila yau, a jiya Talata, ofishin kula da ayyukan agaji na MDD (OCHA), ya yi gargadi game da tsanantar yanayin jin kai a yankin na Barsalogho tun ma kafin aukuwar harin. (Fa’iza Mustapha)