Kamfanin Boeing: zuwa 2043, jiragen saman fasinja na kasar Sin za su ninka fiye da sau 2
2024-08-28 11:01:17 CMG Hausa
Yayin da bangaren sufurin saman kasar Sin ke kara fadada da tafiya da zamani, jiragen saman fasinja za su ninka fiye da sau 2 zuwa 2043, domin cimma karuwar bukatun fasinjoji da jigilar kayayyaki.
Kasuwar sufurin jiragen sama ta kasar Sin a bangarorin fasinjoji da kayayyaki na ci gaba da fadada, bisa bunkasar tattalin arziki da yadda kamfanonin jiragen sama ke tsara a cikin kasar. Hasashe ya nuna cewa, za a samu karuwar bukatar jiragen sama a kasar Sin, lamarin da zai bukaci karin jirage masu amfani da makamashin zamani.
Jiragen saman fasinja na kasar Sin za su karu da kaso 4.1 a kowacce shekara daga 4,345 zuwa 9,740 zuwa shekarar 2043, kana yawan fasinjoji zai karu da kaso 5.9 inda zai zarce matsakaicin matakin na duniya dake kan kaso 4.7. (Fa’iza Mustapha)