Xie Feng: Babu dalilin da zai sa dangantakar Sin da Amurka ta zama irin ta Kyanwa da Bera
2024-08-28 21:29:50 CMG Hausa
Jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya bayyana a ranar Talata cewa, babu dalilin da zai sa alakar Sin da Amurka ta zamto ta samun riba ga bangare daya da samar da asara ga dayan bangaren, kasancewar kasashen biyu sun riga sun kulla alaka mai zurfi, kuma ba za su rabu da juna ba.
Xie ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a dandanlin kasuwanci tsakanin Amurka da Sin karo na shida, wanda mujallar Forbes ta shirya.
Xie ya ce, a wannan duniya mai sarkakiya, neman damammaki aiki ne na bai daya, kuma fadada da zurfafa hadin gwiwarsu ita ce hanya mafi kyau ga ci gaba.
Xie ya kuma jaddada cewa, Sin ba za ta daina yunkurinta na yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje ba, hakan zai samar da damammaki ga Amurka da ma duniya baki daya.
Ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Amurka wajen inganta tattaunawa da sadarwa, da sarrafa bambance-bambance yadda ya kamata, da fadada hadin gwiwar moriyar juna, ta yadda za a daidaita dangantakar da ke tsakanin juna, da kuma ciyar da ita gaba. (Yahaya)