Abokin da ke iya ba ka taimako a lokacin da kake bukata, shi ne aboki na kwarai
2024-08-27 22:32:19 CMG Hausa
Akwai nisan kimanin kilomita dubu 10 tsakanin Kenya da kasar Sin, to, amma ko kun san tsawon lokacin da aka dauka wajen jigilar wani furen rose da aka tsinta daga gonar da ke kasar ta Kenya zuwa kasar Sin?
Allah ya hore wa kasar Kenya albarkatun furanni irinsu Rose, har ma kasar ta kasance kasar da ta fi yawan fitar da furanni zuwa ketare a nahiyar Afirka. Sai dai a baya, a kan shafe tsawon kwanaki uku kafin a kai furannin kasar Kenya kasuwannin kasar Sin, lokacin da ya yi matukar raguwa zuwa sa’o’i 17 kawai a yanzu.
Amma me ya haifar da wannan babban sauyi mai ban mamaki? Amsa ita ce matakan da kasar Sin ta yi ta dauka na inganta hadin gwiwarta da kasashen Afirka ta fannin cinikayya. Idan ba mu manta ba, a watan Nuwamban shekarar 2021, gwamnatin kasar Sin ta sanar da samar da matakai masu sauki kan amfanin gona da ke shigowa daga kasashen Afirka, inda ta rage tsawon lokaci na binciken cututtuka da ma fadada kayayyakin da ake cire musu harajin kwastam da sauransu, matakan da suka fadada hanyoyi zuwa kasuwannin kasar Sin ga amfanin gonar kasashen Afirka, ciki har da furannin kasar Kenya da Avokado da lemo da Abarba da sauransu. Ya zuwa watan Yunin bara, akwai nau’o’in amfanin gona 16 na kasashen Afirka 11 da kasar Sin ta shigo da su kasuwanninta sakamakon matakan, an kuma cire harajin kwastam a kan kaso 98% na kayayyakin da kasar Sin ta shigo daga wasu kasashen Afirka 21.
Ban da haka, kasar Sin ta kuma kafa bikin baje kolin kayayyakin da take shigowa da su kasa da kasa, da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka da musamman ta kafa domin kasashen Afirka, da sauransu, don yayata kayayyakin kasashen Afirka a kasuwanninta.
Cinikin waje na daya daga cikin manyan gishikai uku da ke samar da bunkasar tattalin arziki, don haka ma kullum ake saka batun bunkasa ciniki a matsayin daya daga cikin muhimman fannoni na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Bisa ingantattun matakan da aka ta dauka a gun tarurukan dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashen Afirka ya yi ta bunkasa tare da haifar gaggaruman nasarori, inda a cikin shekaru 15 a jere, kasar Sin ta kasance abokin cinikayya mafi girma ga nahiyar Afirka, a bara kuma, jimillar ciniki a tsakanin sassan biyu har ta kai wani matsayin tarihi na dala biliyan 282.1.
Sakamakon makamancin abin da ya faru gare su a tarihi da ma buri daya da suke neman cimmawa, kasar Sin ta san mene ne aminanta na Afirka ke fatan cimmawa, don haka ma take son raba damammaki da su don tabbatar da hadin gwiwar cin moriyar juna.
Kamar yadda bature kan ce, abokin da ke iya ba ka taimako a lokacin da kake bukata, shi ne aboki na kwarai. Abin haka yake, wanda kuma hakan ya shaida huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka.(Mai zane:Mustapha Bulama)