Karyewar madatsar ruwa a Sudan ta haifar da asarar rayuka a kalla 60 a gabashin kasar
2024-08-27 09:53:03 CMG Hausa
Rahotanni daga kasar Sudan na cewa, madatsar ruwa ta Arbaat dake jihar Red Sea ta gabashin kasar ta karye, lamarin da ya haifar da ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar rasuwar a kalla mutane 60, yayin da kuma daruruwan mutane suka bace. Majiyoyin gwamnatin kasar sun ce ibtila’in ya auku ne a ranar Lahadin karshen makon jiya.
Da yake tsokaci game da faruwar lamarin, shugaban hukumar lura da albarkatun ruwa ta jihar Omer Issa Tahir, ya ce ballewar dam din ya haifar da ambaliyar ruwa da ta mamaye daukacin kauyukan dake kusa da tashar ruwa ta Port Sudan. Jami’in ya bayyana matukar bukatar samar da tallafin gaggauwa ga al’ummun dake daura da kauyukan, yana mai bayyana damuwa game da yadda kwari masu hadari, ciki har da kunamu da macizai ke cizon mutanen da suka haye kan tsaunuka domin tsira daga ambaliyar.
Tahir ya ce muhimmin mataki a yanzu shi ne kwashe wadanda ambaliyar ta yiwa kawanya, a gabar da masu aikin ceto ke aiki tukuru domin kaiwa gare su.
Kafofin watsa labaran wurin sun ce, ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya sanya tarin baraguzai ture iyakar dam din, lamarin da ya haifar da ambaliyar da ta mamaye kauyukan dake kusa, tare da haifar da babban kalubale ga aikin ceton al’umma.
Dam din Arbaat, na da nisan kilomita kusan 20 daga arewa da tashar ruwan Port Sudan, yana kuma iya daukar ruwa har kyubik mita miliyan 25, kuma da shi birnin Port Sudan ya dogara wajen samar da ruwa ga al’umma. (Saminu Alhassan)