Tawagar jiragen rundunar sojin saman kasar Sin ta tafi Masar domin halartar wani bikin nune-nune
2024-08-27 11:09:58 CMG Hausa
Tawagar jirage 8 ta rundunar sojin saman kasar Sin (PLA), ta tashi jiya Litinin, daga wani filin jirgin sama dake arewa maso yammacin kasar Sin, inda ta nufi kasar Masar domin halartar bikin nune-nune fasahar sarrafa jirage, wanda zai gudana daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Satumba.
Tawagar jiragen ta hada da jirgin Y-20, babban jirgi da aka kera a kasar Sin domin sufuri da kuma jiragen yaki na J-10 guda 7, daga tawagar jirage mai nuna fasahar sarrafa jirgin sama ta salo daban daban a sararin samaniya ta Bayi Aerobatic.
Kakakin rundunar sojin saman kasar Sin Xie Peng, ya ce wannan shi ne karon farko da tawagar ta Bayi Aerobatic za ta nuna fasahar a wata kasa dake nahiyar Afrika, haka kuma ita ce tafiya mafi nisa da jiragen suka yi zuwa wata kasa.
Yayin da suke can, jiragen za su yi shawagi a saman jerin Pyramid-Dalar Masar. Kuma wannan ne karo na farko da jirgin Y-20 ya tafi ketare. (Fa’iza Mustapha)