Sakatare janar na MDD ya yi tir da hare-haren da aka kai lardin Balochistan na Pakistan
2024-08-27 11:01:20 CMG Hausa
Sakatare-janar na MDD Antonio Guterres ya yi suka da kausasan kalamai kan hare-haren da aka kai lardin Balochistan na kasar Pakistan a jiya Litinin.
Yayin wani taron manema labarai, kakakin sakatare-janar din Stephane Dujjaric ya ruwaito Antonio Guterres na bayyana hare-hare kan fararen hula a matsayin wanda ba za a lamunta ba.
Antonio Guterres ya kuma jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu, yana mai kira ga gwamnatin Pakistan ta gudanar da bincike domin tabbatar da hukunta wadanda ke da hannu.
Mutane a kalla 53, ciki har da jami’an tsaro ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata
sanadiyyar jerin hare-haren da aka kai lardin Balochistan dake kudu maso yammacin Pakistan, a jiya Litinin. (Fa’iza Mustapha)