logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya nada sabbin shugabannin hukumomin leken asiri na kasa

2024-08-27 10:14:03 CMG Hausa

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya nada sabbin shugabannin hukumomin leken asiri na kasa, wato hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS, da na hukumar leken asiri ta kasa NIA, a wani mataki na shawo kan kalubalen tsaro dake addabar kasar.

Wata sanarwar gwamnati ta ce, shugaban na Najeriya ya nada Mohammed Mohammed, a matsayin sabon shugaban hukumar NIA, bayan ya shafe tsawon lokaci yana aikin diflomasiyya karkashin hukumar tun fara aiki cikin ta a shekarar 1995. Ana hasashen kwarewarsa za ta zaburar da ayyukan hukumar yadda ya kamata.

A daya bangaren kuma, shugaba Tinubu ya nada Adeola Ajayi, a matsayin sabon shugaban hukumar DSS, bayan ya shafe tsawon lokaci yana aiki a hukumar. Ajayi na da kwarewa da ake ganin za ta iya taimakawa yakin da kasar ke yi da matsalolin tsaro.

Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin jagororin biyu da su gudanar da ayyukan su bisa sanin ya kamata, ta yadda za su inganta ayyukan hukumomin na wanzar da tsaron Najeriya. (Saminu Alhassan)