Yawan ribar da masana’antu masu matsakaicin kudin shiga suka samu ya karu da kashi 3.6% a farkon watanni 7 na bana
2024-08-27 16:20:01 CMG Hausa
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ba da rahoto a yau Talata, cewa daga watan Janairu zuwa Yuli na bana, yawan ribar da masana’antu masu matsakaicin kudin shiga suka samu ya kai dalar biliyan 575, wanda ya karu da kashi 3.6% bisa na makamancin lokaci na bara.
Daga cikinsu, masana’antu masu dogaro da kimiyyar zamani suna sahun gaba, inda a tsawon wannan lokaci, yawan ribar da suka samu ta karu da kashi 12.8% bisa na makamacin lokacin bara.
Ban da wannan kuma, yawan ribar masana’antun samar da na’urori ya karu da kashi 6.1% bisa na makamancin lokaci na bara, wanda hakan ya nuna dorewar karuwarsa. (Amina Xu)