Wang Yi da Jake Sullivan sun gudanar da sabon zagaye na muhimmin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka
2024-08-27 20:43:44 CMG Hausa
Wang Yi, darektan ofishin kwamitin koli kan harkokin waje, ya gudanar da wani sabon zagaye na muhimmin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka tare da mashawarcin shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan a Yau Talata a birnin Beijing.
Wang, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya bayyana cewa, tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a birnin San Francisco, shi ne ainihin aiki na wannan sabon zagaye na muhimmin tattaunawa tsakin Sin da Amurka.
Sullivan na ziyarar kwanaki uku ne a babban birnin kasar Sin don gudanar da sabon zagaye na muhimmin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka. (Yahaya)