Muhalli mai kyau na kasar Sin ya sake dawo da giwaye
2024-08-27 22:21:36 CMG Hausa
A kwanaki biyu da suka gabata, giwaye irin na Asiya daga yankin Xishuangbanna dake lardin Yunnan na kasar Sin sun sake yin yawo daga wajen yankin kiyaye dabbobin daji. Bisa kariyar da ‘yan sanda da masu sa ido suka ba su, giwaye 42 sun yi yawo har sun dawo yankin ba da kariya ga dabbobi. Kamar dai yadda ya faru a shekaru 3 da suka gabata, giwaye irin na Asiya guda 15 sun tafi yin yawo har na tsawon watanni 4, sai dai da taimakon dan Adam suka dawo gidansu.
Akwai tambayar in giwayen suka ci amfanin gonakin da aka shuka a kan hanyar yawonsu, yaya za a yi? Sai dai a duba tsarin inshorar jama’a kan harkokin dabbobin daji da lardin Yunnan ya gabatar karo na farko. A shekarar 2023, sashen sakatariyar kula da yarjejeniyar cinikin kasa da kasa kan dabbobi da shuke-shuken da suka kusan bacewa a doran kasa ya maida wannan tsari a matsayin abin misali. Mataimakin shugaban cibiyar kula da giwaye irin na Asiya na yankin Xishuangbanna Xiong Zhaoyong ya bayyana cewa, bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, an samu jituwa a tsakanin dan Adam da giwaye, don haka mutane sun iya bada kariya ga giwaye.
Yanzu ana kokarin kiyaye muhalli a sassan kasar Sin. An tsaida manufofi kan gyara tsarin kiyaye muhalli a cikakken zama na 3 na majalisar wakilan jam’iyyar kwaminis ta Sin karo na 20 da aka gudanar a kwanakin baya.
Al’amura da dama sun shaida cewa, Sin tana kokarin samun zamanintar da kasa tare da kiyaye muhallin halittu. A nan gaba, Sin za ta kara samar da gudummawa wajen samun ci gaban duniya tare da kiyaye muhalli baki daya. (Zainab Zhang)