logo

HAUSA

Kasar Sin ta nuna rashin gamsuwa da harajin da Canada ta kakaba wa EV

2024-08-27 19:44:20 CMG Hausa

Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin a yau Talata ta bayyana rashin gamsuwa da adawa da kakkausar murya kan matakin da gwamnatin Canada ta dauka na kakaba haraji kan motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin, inda ta bukaci Ottawa da ta gaggauta gyara munanan kurakuranta.

Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin ya ce, wannan matakin kariyar cinikayya na Canada zai kawo cikas ga daidaiton masana’antun duniya da tsarin samar da kayayyaki, da yin illa a tsarin tattalin arzikin duniya da ka’idojin tattalin arziki da cinikayya na duniya.

A ranar Litinin ne dai firaministan Canada Justin Trudeau ya sanar a taron majalisar ministocin tarayyar kasar da aka yi a Halifax cewa, kasar za ta kara harajin shigo da kayayyaki kan motoci masu amfani da lantarki ko EVs kirar kasar Sin daga kashi 6.1 cikin dari zuwa kashi 106.1 bisa dari daga ranar 1 ga Oktoba. (Yahaya)