Shugaban Zanzibar na kasar Tanzaniya, ya ba da lambabin yabo ga tawagar likitocin kasar Sin bisa taimakon da suka baiwa Zanzibar
2024-08-26 21:39:47 CMG Hausa
A yau 26 ga wata, shugaban Zanzibar na kasar Tanzaniya Hussein Ali Mwinyi ya gana da tawagar likitoci ta kasar Sin karo na 33 a fadarsa, inda ya ba da lambobin yabo da takardun shaida na karramawa da tunawa, ga daukacin mambobin tawagar bisa gudunmawar da suka bayar a fannin ba da jinya da kiwon lafiya a Zanzibar.
A wajen bikin ba da lambar yabon, Mwinyi ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin bisa gagarumin gudummawar da ta bayar ga ayyukan ba da jinya da na kiwon lafiya na Zanzibar cikin shekaru 60 da suka gabata, ya kuma yaba wa tawagar likitocin kasar Sin da kwazon aiki da sadaukar da kai. Ya bayyana cewa, tawagar likitocin kasar Sin ba kawai ta yi amfani da fasahar zamani wajen kula da majinyata na yankin ba, har ma ta dauki matakin horar da dalibai da likitoci na Zanzibar, tare da kebe masu hazaka don raya aikin likitancin Zanzibar.
Tun shekarar 1964 ne, kasar Sin take tura tawagogin likitoci zuwa Zanzibar. (Yahaya)