Hamas ta bukaci Isra’ila ta bi manufar tsagaita bude wuta da aka mika mata a watan Yuli
2024-08-26 11:19:37 CMG Hausa
Mamban hukumar siyasa a kungiyar Hamas Izzat al-Risheq, ya fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, wadda ta bukaci Isra’ila da ta bi manufar tsagaita bude wuta da aka mika mata a watan Yuli, wadda mayan abubuwan dake cikinta suka hada da shawarwarin da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar, da kuma wasu kudurori masu nasaba da hakan na kwamitin tsaron MDD.
Sanarwar ta bayyana cewa, tawagar tattaunawa ta Hamas ta riga ta bar birnin Alkahiran Masar a daren jiya Lahadi, bayan da ta gana da bangarorin Masar, da Qatar, da samun samakon tattaunawa.
Sanarwar ta kara da cewa, Hamas na son aiwatar da manufar hade shawarwarin da Biden ya fitar da kuma kudurorin kwamitin sulhu mai nasaba da hakan, ta hanyar cimma babbar moriyar al’ummar zirin Gaza, da kuma hana yakin da yankin ke fama da shi.
Buku da kari, sanarwar ta ce, tawagar Hamas ta jadadda matsayinta, cewa kowace yarjejeniya dole ne ta kunshi tsagaita bude wuta har abada, da janye rundunar soja daga zirin Gaza baki daya, kana al’ummun zirin Gaza su koma gidajensu cikin ’yanci, da sake gina zirin Gaza, da kuma sakin mutanen da ake tsare da su da sauransu.
Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta zirin Gaza ta Falasdinu ta fitar jiya Lahadi, tun bayan barkewar sabon rikici tsakanin Falasdinu da Isra’ila a watan Oktoba na shekarar bara, ayyukan soja da Isra’ila ta gudanar a zirin Gaza, sun riga sun haddasa mutuwar Falasdinawa fiye da dubu 40, kuma fiye da dubu 93 sun ji raunuka. (Safiyah Ma)