logo

HAUSA

An nada sabbin ministoci a kasar Tunisiya

2024-08-26 11:16:48 CMG Hausa

 

Fadar shugaban kasar Tunisiya, ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke cewa shugaban kasar Kais Saied, ya yi garambawul kan gwamnatin kasar, ya kuma nada sabbin ministocinsa a jiya.

Shugaban kasar ya sauya ministoci 19, ciki har da ministan tsaro da na harkokin waje, gami da sakatarorin harkokin kasa 3. Amma sanarwar ba ta fayyace dalilin sauyin ba. Sabbin ministocin sun yi rantsuwar kama aiki a jiyan a fadar shugaban kasar. (Amina Xu)