Li Qiang ya yi kira da a karfafa hadin gwiwar kasa da kasa don bunkasa masana’antar mutum-mutumin inji
2024-08-26 10:26:50 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jaddada bukatar samar da yanayin habaka kirkire kirkiren fasahohi a bude, da tallafawa kamfanonin waje, da cibiyoyin bincike da damar zuba jari a kasar Sin, yayin da ake batu kan ingiza ci gaban masana’antar kera mutum-mutumin inji, karkashin tsarin hadin gwiwar kut da kut na sassan kasa da kasa.
Li, ya yi kiran ne a jiya Lahadi a birnin Beijing, yayin da yake kewayen nazarin abubuwan da aka baje kolin su, a wurin bikin baje-kolin nau’o’in mutum-mutumin inji na kasa da kasa na shekarar 2024.
Ya ce wajibi ne a kafa, tare da amfani da dandalolin hadin gwiwa, domin gudanar da musaya tsakanin masana’antu, da wanzar da daidaito, da gudanar da ayyukan sarrafa hajojin masana’antu lami lafiya, tare da ingiza kirkire kirkiren fasaha a fannin kirar mutum-mutumin inji a matakin kasa da kasa.
Baje-kolin nau’o’in mutum-mutumin inji na kasa da kasa na shekarar 2024, bangare ne na babban taron masu ruwa da tsaki na duniya a fannin mai yini 5, wanda aka bude tun daga ranar Laraba, bisa taken "Hadin gwiwa domin cimma gajiya nan gaba daga kirkirarriyar basira karkashin tasirin sabbin karfi masu inganci". (Saminu Alhassan)