logo

HAUSA

Kim Jong-un ya jagoranci gwajin jirgin sama na yaki maras matuki

2024-08-26 11:05:17 CMG Hausa

 

Babban sakataren jam’iyyar kwadago ta kasar Koriya ta arewa, kana shugaban majalisar kula da harkokin kasar Kim Jong-un, ya jagoranci aikin gwajin jirgin saman yaki maras matuki, wanda cibiyar nazarin jirgin sama maras matuki ta kwalejin binciken kimiyyar tsaron kasar ta gudanar a ranar 24 ga wata.

Rahotanni na cewa, Kim Jong-un ya nazarci jiragen da aka yi bincike da kuma kerawa a kwanan baya, wadanda ke da amfani wajen kai hari a doron kasa da sararin teku. Yayin aikin gwajin, jiragen saman samfura daban-daban sun bi hanyoyin da aka tanada, don tabbatar da kai hari daidai a wurare daban daban.

Rahotanni sun nuna cewa, Kim Jong-un ya bayyana nazari gami da kera mabambantan jiragen saman yaki marasa matuka, da kara karfinsu na yaki, a matsayin wani muhimmin mataki na daura damarar yaki. Ya kuma bukaci a kara karfin nazari, da kera irin wadannan makamai, da girke su a rundunar sojan kasar. (Amina Xu)