logo

HAUSA

Sefeton 'yan sandan Najeriya ya karbi dalibai likitoci da aka ceto daga hannun 'yan bindiga

2024-08-26 09:10:41 CMG Hausa

Sefeto janaral na 'yan sandan Najeriya Mr Kayode Egbetokun ya tabbatar da kashe wani jagoran masu garkuwa da mutane sannan kuma an kama wasu mutum biyu yayin da ake kokarin ceto daluban nan 20 masu nazarin aikin likita da aka yi garkuwa da su kwanakin da suka gabata.

Ya tabbatar da hakan ne ranar Lahadi 25 ga wata a hedikwatar rundunar 'yan sanda ta kasa dake birnin Abuja lokacin da yake mika daliban da aka ceto ga shugabanin jami'o'insu, inda ya kara da cewa, ana ci gaba kuma da tsare 'yan bindigar da aka kama.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.