Liu Ying: Kiyaye yara shi ne alhakinmu, kuma nauyi ne dake bisa wuyan mu
2024-08-26 20:53:08 CMG Hausa
Liu Ying, wadda ke aiki a hukumar gabatar da kararraki ta gundumar Le’an dake lardin Jiangxi dake kudu maso gabashin kasar Sin, ta koyi Sinanci a lokacin da take karatu a jami'a, amma bayan ta kammala karatu a jami’a, sai aka shigar da ita hukumar gabatar da kararraki, kuma ta zama ’yar sanda a fannin shari’a, a yanzu haka ta shafe shekaru 12 tana wannan aikin kuma ta himmatu wajen kare lafiyar kananan yara.
Liu Ying ta bayyana cewa, asalin aikinta na kare yara kanana, shi ne lokacin da take taimakawa kan binciken wani laifin da wata karamar yarinya ta aikata, abubuwan da suka faru kan wannan yarinya sun burge ta sosai. Liu Ying ta ce ba za ta iya mantawa da yadda yarinyar ta yi kuka ba, kuma a lokacin ne zuciyarta ta ji zafi sosai. Wannan yarinyar ya kasance misali ne na rashin samun ilimin jima’i da ilimin kariyar kai, sabili da haka, ta yanke shawarar yin duk abin da za ta iya ga yara.
A watan Oktoban shekarar 2018, hukumar gabatar da kararraki ta koli ta kasar Sin ta kaddamar da wata takarda, inda ta ba da shawarar kara kyautata tsarin hana cin zarafi, da karfafa sa ido, da duba yadda ake aiwatar da tsarin da ya dace na hana cin zarafi a fannin jima’i, da karfafa kulawa, da dubawa game da aiwatar da tsare-tsaren da suka dace don hana cin zarafin jima’i a makarantu, da kuma yanke hukunci mai tsanani ga mutanen da suka keta doka da ka’ida da dai sauransu. Liu Ying ta ba da gudummawa don kafa kungiyar sa kai ta ilmantar da dokoki tare da takwarorinsu na kungiyar kula da harkokin mata da hukumar gabatar da kararraki.
Ita da tawagarta sun gudanar da lakcoci kan kare yara kanana kuma sun bi gida-gida don yada dokar. Baya ga haka, sun rubuta rahoton bincike, wanda ya ba da cikakkun bayanai game da adadin yaran da aka bari a cikin gundumar, da nau’ikan laifukan da suka shafi kananan yara, da kuma wuraren da aka fi gudanar da laifuka da dai makamantansu.
A watan Agusta na shekarar 2020, an kafa kungiyar“’Yar’uwa Liu Ying” a hukumance. A matsayin ta na shugabar kungiyar, Liu Ying ta jagoranci ‘yan kungiyar don yayata ilmin dokoki ta yanar gizo da ma ido da ido, da kafa tsarin samun goyon baya daga wajen al’umma, da ba da tallafi ga yara a dukkan fannoni. Kana sun nemo hanyoyin da suka dace da yara, don koya musu ilmin dokoki.
Baya ga haka, kungiyar na samar da hidima ta kulawa ga kananan yara. Daga cikin su, gidan rediyon FM na “’Yar’uwa Liu Ying” ya samu karbuwa sosai daga yara da ma iyayensu. “Bari mu tattauna tare game da matsalolin da kuke samu a fannin yin mu’ammala tsakanin ku da iyayenku, da kuma matsin lamba da kuke gamuwa da su ta fuskokin karatu da rayuwa, da ma hanyoyin da za mu saukaka shi.” “Bari mu koyi dabarun kare kanmu, da ilmomin da suka shafi zaman rayuwa da dokoki.” “Wadanne irin rudani ko abubuwa ne ba ku fahimta ba a kan hanyarku ta girma?”......“Game da wadannan batutuwa, za ku iya sauraron abin da ‘’Yar’uwa Liu Ying’ ta fada, bari ‘’Yar’uwa Liu Ying’ ta zama ‘mala’ika mai kula da ku’ a gefenku.”
Wadannan shirye-shiryen sun samu karbuwa sosai daga yara da iyayensu. Wata uwa mace cikin godiya ta ce, tana bibiyar gidan rediyon FM na“’Yar’uwa Liu Ying”, a cewarta, abubuwan da ke cikin shirye-shiryen na da ban sha’awa sosai, wanda ya sa ta rage fuskantar rudani a kan hanyar tarbiyyar yara! A cikin shekarar da ta gabata, dangantakarta da danta na kara samun kusanci daga nesa.
Mutane da yawa a gundumar Le’an suna fita waje domin gudanar da aiki a sauran yankuna, don haka, yara da yawa suna kasancewa tare da kakanninsu a gida.
Liu Ying ta gano cewa, babban dalilin da ya sa yaran da ake bari a baya, suka fi zama rukunin da ya fi aikata laifuka, da ma wanda aka fi cin zarafinsu, shi ne baya ga cewa iyayensu sun dade ba su zama tare da su, wanda ke haifar da rashin kulawa da suke samu, wani muhimmin dalili na daban kuma shi ne ba su da ra’ayi na sani, fahimta, kiyaye, da kuma amfani da dokoki.
Yadda za a sa yara masu shekaru daban-daban su yi sha’awar ilimin dokoki, ta kasance tambaya da Liu Ying ta yi tunani a kai.
Liu Ying ta taba gamuwa da wani lamari game da Beibei. Yaro ne da aka bari wanda iyayensa suka raina saboda tsagewar lebe da baki a lokacin haihuwarsa, kuma kakanninsa ne suka rene shi. Daga baya kuma an kama shi da laifin yin sata, saboda rashin kulawar sa wajen yin abokai. Bayan yin mu’ammala da ba shi shawarwari kan tunani kai-da-kai, Beibei ya sauya daga zama mai son zuciya da farko, har ya fara gane kuskurensa. Daga baya, Beibei ya tafi aiki a wani shagon gyaran kayan gida. Sai dai babu wanda ya yi tsammanin cewa bayan ’yan watanni, Liu Ying da Beibei za su sake haduwa a gidan yari, a wannan karon, an kama Beibei da laifin gyara wani babur da aka sace.
Liu Ying ta fada cikin tunani, ta yaya za a hana yara aikata laifi? Ko shakka babu, dogaro da ba da shawarwari kan tunani kawai ga yara bai iso ba, ya kamata a hada karfi na iyalai, makarantu, sassan shari’a, da sauran bangarorin don kafa wani tsarin kare yara.
Liu Ying da ’yan kungiyarta su yi amfani da yanar gizo don yada ilmin dokoki, kana da gudanar da lakcoci na shari’a, da gasar ilimin dokoki ga daliban sakandare. Har ila yau, sun kafa kujeru guda 261 na jami’an tuntuba a makarantu, don tattara burin da daliban suke fatan cimmawa, da ma ba su shawarwari na tunani. Ban da wannan kuma, sun tsara wasan kwaikwayo don yada ilimin dokoki ta hanyar da yara suke so.
Yanzu, ma’aikatan kungiyar “’Yar’uwa Liu Ying” sun fadada daga gundumar Le’an har zuwa birnin Fuzhou, don gudanar da aikin kare yara tare. Ya zuwa yanzu, an riga an kafa kungiyar“’Yar’uwa Liu Ying” guda 12 a birnin, da ma ofisoshin aiki na“’Yar’uwa Liu Ying” 485 a makarantun firamare da na sakandare.“’Yar’uwa Liu Ying” sannu a hankali ta zama daidai da kalmar “kauna da kariya” a cikin zukatan yara.