Isra’ila ta kaddamar da hare-hare kan Lebanon, inda Hezbollah ta mayar da martani mai karfi
2024-08-25 17:11:03 CMG Hausa
Wani rahoton kafar yada labarai na AP ya ruwaito cewa, Isra’ila ta kaddamar da jerin luguden wuta masu karfi, kan kudancin Lebanon da sanyin safiyar yau Lahadi, cikin wani mataki da ta kira na dakatar da mayakan kungiyar Hezbollah, lamarin dake barazanar fadada yaki a yankin, wanda kuma ka iya murkushe kokarin da ake na tsagaita wuta a Gaza.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce kungiyar Hezbollah na shirin kaddamar da hare-haren roka da makamai masu linzami kan Isra’ila. Kungiyar mai samun goyon bayan Iran ta yi alkawarin daukar fansa kan kisan da Isra’ila ta yi wa wani babban kwamandanta a karshen watan da ya gabata.
An bayar da rahoton jin karar hare-hare ta sama a baki dayan yankin arewacin Isra’ila, kuma filin jirgin sama na kasa da kasa na Ben-Gurion na Isra’ilar, ya fara karkatar da akalar jiragen da ya kamata su sauka a nan, tare da dage tashin jirage. Haka kuma, ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant, ya ayyana matakin ta baci na tsawon sa’o’i 48.
Kafar yada labarai ta AP ta ruwaito cewa, jim kadan bayan nan, kungiyar Hezbollah ta sanar da kaddamar da hari kan Isra’ila da jirage marasa matuka masu yawa, a matsayin matakin farko na martani kan kisan Fouad Shukur, wani babban kwamandan kungiyar, yayin wani hari da Isra’ila ta kai yankin kudancin birnin Beirut.
Hare-haren na zuwa ne yayin da Masar ke karbar bakuncin wani sabon zagayen tattaunawa da nufin kawo karshen yakin Isra’ila kan kungiyar Hamas, wanda ya shiga wata na 11. Kungiyar Hezbollah dai ta ce za ta dakatar da kai hare-hare, idan aka cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta. (Fa’iza Mustapha)