Jakadan Sin dake Najeriya: Taron kolin FOCAC na shekarar 2024 zai samar da kyakkyawar dama ga Sin da Afirka
2024-08-25 17:08:31 CMG Hausa
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai, ya ce gudanar da taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka(FOCAC) zai samar da kyakkyawar dama ga Sin da kasashen Afirka wajen kara hadin kai, da zurfafa hadin gwiwa, da zamanintar da kasashen, da kuma raya kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da Afirka.
Yu Dunhai ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da wakilin kafar CGTN, lokacin da yake tsokaci dangane da taron koli na dandalin FOCAC na shekarar 2024 da za a gudanar a birnin Beijing.
Ya kara da cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kana kasancewarta daya daga cikin kasashe masu tasowa na duniya, tana dora muhimmanci kan hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa. Ya ce cikin shekaru 24 bayan kafuwar dandalin FOCAC, karkashin tsarin dandalin, Sin da kasashen Afirka sun yi hadin gwiwa cikin nasara a fannoni daban daban, lamarin da ya amfanawa jama’ar bangarorin biyu baki daya.
Haka zalika, Yu Dunhai ya jaddada cewa, Najeriya babbar kawa ce ta kasar Sin a nahiyar Afirka, kuma ya yi imanin cewa, taron kolin dandalin FOCAC da za a gudanar a wannan karo zai samar da wata muhimmiyar dama ga Sin da Najeriya, ta yadda za su karfafa hadin gwiwa da daukaka dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab Zhang)