logo

HAUSA

Cibiyar Africa CDC ta yi gargadin game da karuwar masu kamuwa da cutar kyandar biri

2024-08-25 16:44:43 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da yaki da yaduwar cututtuka ta Afrika wato Africa CDC, ta yi gargadi game da samun karuwar masu kamuwa da cutar kyandar biri, da karancin gano masu kamuwa da ita da ma karuwar mace-mace a sanadinta, tana mai bayyana hakan a matsayin kalubalen dake yi wa nahiyar tarnaki, a kokarinta na shawo kan cutar, yayin da ake kara samun masu kamuwa da ita.

Darakta janar na cibiyar Jean Kaseya, ya bayyana cikin sabon bayanin da ya fitar kan yanayin cutar a kasa da kasa, a ranar Juma’a cewa, kalubalen na da alaka da yaduwar cutar cikin sauri zuwa wasu sabbin kasashe, da bambanci don gane da matakan shawo kanta, yayin da ake matukar bukatar inganta hadin gwiwa.

Ya kara da gargadin game da karuwar mace-mace sanadiyyar cutar wanda ya ce galibi na tsakanin kaso 3 zuwa 4, yana mai cewa, alakar cutar da cutar kanjamau, wani karin damuwa ne ga nahiyar Afrika.

Har ila yau, ya ce ta hanyar hada hannu da kasashen Afrika, WHO da sauran abokan hulda da kuma amfani da karfin AU a bangaren siyasa da manufofi wajen tunkarar cutar, cibiyar na taimakawa kasashen Afrika a ayyukansu na shirin dakilewa da tunkarar cutar.

Alkaluma daga cibiyar Afrika CDC sun nuna cewa, daga farkon shekarar 2024 zuwa ranar 23 ga watan Augusta, jimilar mutane 21,466 ne ake tsammanin sun kamu da cutar, kuma an samu rahoton mutuwar 591, daga kasashe 13 mambobin Tarayyar Afrika (AU).

Kasashen na AU da kawo yanzu suka bada rahoton bullar cutar sun hada da Burundi da Kamaru da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Jamhuriyar Congo da Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Gabon da Liberia da Kenya da Nijeriya da Rwanda da Afrika ta Kudu da kuma Uganda. (Fa’iza Mustapha)