logo

HAUSA

Darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa a tarayyar Najeriya ya ajiye aikinsa

2024-08-25 15:40:25 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din darakta janar na hukumar leken asirin kasar Alhaji Ahmed Rufa`i.

Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya Asabar 24 ga wata a birnin Abuja, shugaba Tinubu ya yi wa tsohon daraktan fatan alheri a dukkan al`amuran da ya sanya a gaba.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A jiya Asabar ne dai Alhaji Ahmed Rufa`i ya sanar da ajiye mukamin nasa bayan ya kammala wata ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

Ya dai kasance a wannan mukami ne tun a shekara ta 2018 zamanin gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari, wanda bayan karewar wa`adin sa aka kara masa lokaci a shekarar 2021.

Mai shekaru 71, tsohon darkatan leken asirin na kasa ya taba kasancewa babban mataimaki na musamman ga tsohon shugaba Muhamadu Buhari a 2015.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Alhaji Ahmed Rufa`i ya ce lokaci ya yi da rya kamata ya janye jiki domin baiwa matasa dama, kasancewa akwai matasa da da yawa masu kwazo da aka horas wadanda za su iya baiwa kasa gudummowa, amma duk da haka abokantakarsa da shugaban kasa za ta ci gaba da gudanuwa ta hanyar ba shi shawarwari a duk lokacin da ya kamata, musamman a kan batun tsaron kasa.

Ya mika godiyarsa bisa irin hadin kan da shugaban kasa ya ba shi a tsawon watanni 15 da ya shafe yana aiki da shi. (Garba Abdullahi Bagwai)