logo

HAUSA

Shugaban gasar Olympics ta Paris 2024 ya aika da wasikar godiya ga shugaban CMG

2024-08-24 15:40:51 CMG Hausa

Tony Estanguet, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics da wasannin Olympics na masu bukatu na musamman na Paris na shekarar 2024, ya rubuta wa shugaban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko CMG, Shen Haixiong wasika, don taya CMG murna bisa yadda ya nuna bajintar bayar da rahotanni da watsa shirye-shiryen wasannin na Paris na 2024, ya kuma gode wa CMG bisa goyon baya da ya baiwa kwamitin shirya gasar.

A cikin wasikar nasa, Estanguet ya bayyana cewa, hadin gwiwa tsakanin CMG da kwamitin shirya gasar ta Paris na 2024 ta taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar wasannin na Olympics. Yadda CMG ya bayar da rahoto da watsa shirye-shiryen gasar Olympics ta Paris ta 2024, ya jawo hankulan jama'a ba kawai daga masu kallo da sauraro Sinawa ba, har ma da jama'ar duniya ga wasannin.

Estanguet ya ce ya gamsu da kwarewar CMG wajen bayar da rahoto da watsa wasannin Paris na shekarar 2024 a dukkan dandamali. Yana fatan CMG zai yi irin wannan gagarumin aiki yayin wasannin Olympics na masu bukatu na musamman na lokacin zafi na 2024 wanda za a fara ranar 28 ga Agusta. (Yahaya)