logo

HAUSA

Mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan zai ziyarci kasar Sin

2024-08-24 16:20:51 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Asabar cewa, a bisa gayyatar memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma daraktan ofishin hukumar kula da harkokin waje na kwamitin koli, Wang Yi, mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan, zai ziyarci kasar Sin daga ranar a 27 zuwa ta 29 ga Agusta. Kuma bangarorin biyu za su gudanar da wani sabon zagaye na muhimmin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka. (Yahaya)