Xi Jinping ya zanta ta wayar tarho da firaministan Birtaniya
2024-08-23 20:50:15 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da firaministan Birtaniya Keir Starmer da yammacin Juma’ar nan, bisa gayyatar da firaministan ya yi masa.
Yayin zantawar ta su, Xi Jinping ya taya Starmer murnar kama aiki a matsayin firaminista, yana mai cewa Sin da Birtaniya mambobin dindindin ne a kwamitin tsaron MDD, kana manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya. Kaza lika, ya dace sassan biyu su rika kallon dangantakar su bisa mahanga ta dogon lokaci, kuma daga dukkanin fannoni, kana su martaba matsayin kawancensu, su karfafa tattaunawa da hadin gwiwa, su kuma amfani kan su da ma duniya baki daya ta hanyar rungumar manufofin cimma moriyar junan su.
Shugaba Xi ya ce Sin a shirye take ta ingiza cikakken tsarin farfado da kan ta mai salon zamanantarwa irin na Sin, tare da bin tafarkin samar da ci gaba cikin lumana, kana tana fatan bangaren Birtaniya ma zai rika kallon Sin bisa gaskiya da hangen nesa. Yayin da a nata bangaren Sin ta shirya shiga duk wata tattaunawa bisa daidaito tare da Birtaniya, bisa martaba juna, da cimma fahimta da amincewa da juna, tare da mayar da burin cimma moriyar juna jigon alakar sassan biyu.
Daga nan sai ya bayyana shirin Sin na karfafa matakan tafiya tare don samar da ci gaba daga dukkanin fannoni tare da bangaren Birtaniya, da fadada hadin gwiwa a fannoni kamar na hada hadar kudade, da samar da ci gaba maras gurbata muhalli, da cin gajiyar kirkirarriyar basira ko AI, da kuma zurfafa musayar al’ummun sassan biyu. (Saminu Alhassan)