Mukadashin shugaban Afirka ta kudu: Sabon gwamnatin kasar za ta ci gaba da daukar manunfar sada zumunci da Sin
2024-08-23 12:08:23 CMG Hausa
Mukadashin shugaban kasar Afirka ta kudu Paul Mashatile ya bayyana a jiya Alhamis cewa, sabon gwamnatin kasar za ta ci gaba da manufarta ta sada zumunci da kasar Sin, yana mai fatan kara hadin gwiwa da Sin a bangaren tattalin arziki da cinikayya da al’adu da sauransu, ta yadda za a gaggauta bunkasa huldar kasashen biyu.
Paul Mashatile ya karbi takardar nadin sabon jakadan Sin dake Afirka ta kudu Wu Peng a wannan rana, inda ya ce, kasashen biyu na da dankon zumunci na dogon lokaci, kuma kasarsa na godiya ga taimakon da Sin ta dade take baiwa ga bunkasuwarta.
A nasa bangare, Wu Peng ya ce, huldar kasashen biyu ta shiga matsayi mai kyau, kiyayewa da kuma raya huldar ya dace da muradun kasashen biyu, lamarin da zai taka rawa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya. Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasar don gaggauta mu’ammala da hadin gwiwa a duk fannoni, ta yadda za a kafa kyakkyawar makoma mai kyau ta bai daya cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)