Kasar Sin ta harba sabon tauraron dan Adam na sadarwa
2024-08-23 10:58:19 CMG Hausa
A jiya Alhamis ne kasar Sin ta aika da sabon tauraron dan Adam na sadarwa zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba kumbuna na Wenchang dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin.
An harba tauraron dan adam na ChinaSat 4A ne da karfe 8 da mintuna 25 na daren jiya Alhamis, bisa agogon Beijing na Sin, ta wani nau’in rokar dakon kaya ta Long March-7 da aka inganta shi.
Tauraron dan adam din zai samar da hidimomin da suka shafi sautin murya, bayanai, da ayyukan watsa shirye-shirye na rediyo da talabijin.
Wannan shi ne aikin dako zuwa sararin samaniya karo na 532 na rokokin Long March. (Yahaya)