Sin: Shawarwarin tsagaita bude wuta da daidaita matsala a siyasance hanya daya kadai da za a iya bi domin warware batun Palasdinu da Isra’ila
2024-08-23 12:06:21 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya ba da jawabi a taron tattaunawa kan batun Palasdinu da Isra’ila da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a jiya 22 ga wata, inda ya nanata cewa, karfin tuwo ba zai haifar da komai ba sai asarar rayukan mutane, kuma ba zai zama sharadi mai kyau wajen kubutar da mutanen da aka tsare da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Isra’ila ba. Tsagaita bude wuta da daidaita matsala a siyasance su ne hanya daya kadai da za a iya bi domin magance wannan matsala.
A cewarsa, Sin ta kalubalanci Isra’ila da ta dakatar da duk wani matakin soja da ta dauka a yankin Gaza, da dakatar da daukar matakan da za su tsanantar da halin da ake ciki a wurin. Sin kuma ta nemi kasashe wadanda suke ba da muhimmin tasiri ga yankin da su sauke nauyin dake bisa wuyansu cikin sahihanci, don sa Isra’ila ta hanzarta dakatar da matakin soja a yankin Gaza, da ma daina yiwa jama’a kisan gila. Sin na fatan hadin kai da al’ummar duniya don taka rawar gani wajen kwantar da yake-yake a yankin tun da wuri, da sassauta bala’in jin kai da tabbatar da “manufar kafa kasashe biyu”, wato kasar Palasdinu da Isra’ila da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya. (Amina Xu)