Shugaban IAEA ya ce zai ziyarci tashar nukiliyar Kursk kan zargin harin jirgin sama mara matuki
2024-08-23 10:23:45 CMG Hausa
Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA ya fada jiya Alhamis cewa, zai ziyarci tashar samar da makamashin nukiliya ta Kursk ta kasar Rasha a mako mai zuwa domin tantance halin da ake ciki bayan Rasha ta sanar da hukumar yunkurin kai hari a cibiyar da safiyar ranar.
Babban darektan hukumar ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, inda ya ce zai tantance halin da ake ciki a wurin tare da tattauna hanyoyin da za a bi don ci gaba da gudanar da ayyukan da ake bukata wajen tantance yanayin tsaron nukiliya da yanayin tsaro na tashar ta Kursk a ziyararsa da zai kai. (Yahaya)