logo

HAUSA

Sin ta kira taron binciken manufofin gaggauta aikin raya yankin yammacin kasar

2024-08-23 15:39:54 CMG Hausa

 

Yau Juma’a, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira wani taron bincike kan manufofin dake da alaka da gaggauta aikin raya yankin yammacin kasar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron.

Taron ya nuna cewa, raya yankin yammacin Sin wata muhimmiyar manufa ce da kwamitin tsakiyar ya tsayar, ya kamata a fahimci burin kwamitin da matsayin wannan aiki wajen zamanintar da al’ummar Sinawa, da kuma mai da hankali kan kiyaye muhalli tare da bude kofa da samun bunkasuwa mai inganci da ma gaggauta kafa sabon hali na samun bunkasuwa da daga karfin yanki na samun bunkasuwa mai dorewa. (Amina Xu)