logo

HAUSA

Firaministan Kasar Sin: Kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa aminiyar Belarus

2024-08-23 10:16:15 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da kasar Belarus domin tabbatar da goyon bayan juna wajen kare muhimman moriyar juna, da kuma kasancewa aminan juna na gaskiya da kyautata hulda tsakanin juna.

Li ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da firaminstan kasar Belarus Roman Golovchenko. Inda ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da kasar Belarus domin aiwatar da muhimman matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da tabbatar da goyon bayan juna wajen kiyaye muradunsu, da zama aminan juna na kwarai kuma abokan hulda na gari, da kiyaye bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a babban mataki, da zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban, da sa kaimi ga yunkurin zamanantarwa na juna.

Ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta karfafa tuntuba da hadin gwiwa da kasar Belarus a MDD, da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da sauran shirye-shirye na bangarori daban daban, da sa kaimi ga aiwatar da hadin gwiwa na hakika, da gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil'Adama tare.

A nasa bangaren, Golovchenko ya ce, bisa jagorancin manyan tsare-tsare na shugabannin kasashen biyu, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba a cikin 'yan shekarun nan, inda ya kara da cewa, kasar Belarus tana son ci gaba da kasancewa aminiya kuma abokiyar huldar kasar Sin, tare da mutunta ka'idar Sin daya tak, tana kuma nuna goyon baya ga matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka shafi yankunan Hong Kong, Xinjiang da Xizang. (Yahaya)