Yawan sabbin kamfanonin da ‘yan kasuwan ketare suka zuba jari ya karu da 11.4% tsakanin Janairu zuwa Yulin bana
2024-08-23 16:11:51 CMG Hausa
Bayanin da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fidda ya nuna cewa, cikin watanni 7 farko na bana, adadin sabbin kamfanonin da ‘yan kasuwan ketare suka zuba jari, wadanda aka kafa a kasar Sin ya karu da kaso 11.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.