logo

HAUSA

An kara kudin yin fasfo a Najeriya

2024-08-22 09:14:31 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da karin kudin yin fasfo ga ’yan kasar.

Da yammacin jiya Laraba ne gwamnatin ta fito da sabon farashin nau’ikan fasfuna cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar shige da fice ta kasa Mr. Kenneth Udo ya rabawa manema labarai a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kamar dai yadda yake kunshe cikin sanarwar, gwamnati ta yanke shawarar karin farashin ne da zummar kara daga matsayi da kimar fasfunan kasar a idon duniya.

Sanarwar ta kara bayanin cewa, gwamnati ba ta yi karin ba ne domin takurawa jama’a illa kawai yanayi da ta duba wanda kuma ya nuna sai lallai an yi karin farashi.

Sabon farashin yin fasfo din zai fara ne daga 1 ga watan gobe na Satumba, amma wannan karin bai shafi ’yan Najeriya da suke zaune a kasashen waje ba.

Yanzu dai a sakamakon sabon tsarin, ga masu bukatar yin fasfo mai shafuka 32 wanda kuma yake da wa’adin karewa na shekaru 5 za a biya naira dubu 50 ne maimakon dubu 35 da ake biya baya, sai kuma fasfo mai shafika 64 mai wa’adin tsawon shekaru 10 za a biya naira dubu 100 ne maimakon dubu 70 da ake biya a baya.

Hukumar shige da ficen ta Najeriya ta kuma bukaci ’yan Najeriya da su karbi wannan canji da zuciya guda, sannan kuma ta kara jaddada kudurinta na kyautata ayyukan ta domin biyan bukatun ’yan kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)