logo

HAUSA

Hadin Kan Sin Da Afrika A Bangaren Kiwon Lafiya Zai Ci Gaba Da Samun Nasarori

2024-08-22 22:13:03 CMG Hausa

DAGA MINA

“Da na bude kofa da safe, sai na ga (maras lafiya)sun yi dogon layi suna jira, don neman samun tallafin kiwon lafiya daga wajenmu, abin da ya bayyana amincewarsu da ni da kuma tawagar likitoci da Sin ta tura musu.” Malama Zhang Youming mai shekaru 91 da haihuwa ce ta gaya min haka yayin da na ziyarce ta a birnin Changsha na tsakiyar kasar Sin a kwanan baya. Ta nuna min wani hoto, ta yi murmurshi ta waiwayi abubuwan da suka faru shekaru 60 da suka gabata, yayin da take ba da taimakon kiwon lafiya a Aljeriya.

A shekarar 1963, jim kadan bayan kasar Aljeriya ta samu ‘yancin kai bayan yake-yake na tsawon shekaru 10, tsarin kiwon lafiyarta ya fuskanci kalubale matuka, don haka gwamnatin kasar ta yi kira ga kasashen duniya da su ba ta taimako. Nan da nan kasar Sin ta tura wata tawagar likitocinta mai mambobi 13 zuwa kasar. A matsayin likita mai kula da mata da mata masu juna biyu Zhang Youming tana daya daga cikinsu. To, daga wannan lokaci, a karon farko tawagar likitocin kasar Sin ta fara gudanar da aiki a Afrika. A cikin wa’adin aikinta na tsawon shekaru 2 da rabi, Zhang Youming ta yi tiyata fiye da sau dubu. Zhang ta tuna da cewa, akwai wata mace mai juna biyu da ta shiga mawuyancin hali yayin haihuwa, daga bisani ta haifi jaririnta lami lafiya karkashin kulawarta, lamarin da ya sa wannan mace ta radawa danta suna “Basine”, saboda tana ganin cewa, likitar Sin ce ta ceci rayuwarta da ta danta.

Tun daga shekarar 1963, likitoci masu dimbin yawa kamar Zhang Youming sun taba ko suna aiki a kasashen Afrika, sun yi kokarin samar da gudummawar jinya har wasunsu sun sadaukar da rayukansu.

Bangaren kiwo lafiya wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwar Sin da Afrika. Kuma turawa kasashen Afrika tawagogin ba da tallafin kiwon lafiya, wani sashi ne na hadin gwiwar Sin da Afrika a bangaren kiwon lafiya. Ban da wannan kuma, Sin ta taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen kiwon lafiya 25 a Afirka, ciki hadda hedkwatar cibiyar magance cututuka masu yaduwa ta Afrika ta AU, da asibitin Bobo-Dioulasso na Burkina Faso da dai sauransu. Kazalika ta samarwa kasashen Afrika tallafin alluran rigakafi kimanin miliyan 240, matakin da ya taimakawa kasashen dake da bukata wajen samun isassun alluran.

Bisa kokarin da likitocin Sin suke ta yi, ba shakka, zumunci a tsakanin Sin da kasashen Afirka na ta karfafa. Hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuskar kiwon lafiya zai ci gaba da samun nasarori a nan gaba, duba da cewa suna kokarin kafa kyakkyawar makomarsu ta bai daya a wannan bangare. (Mai zane da rubutu: MINA)