logo

HAUSA

‘Yan wasa ‘yan gudun hijira sun kafa tarihi yayin gasar Olympic

2024-08-22 20:42:09 CMG Hausa

Tun daga lokacin farko da tawagar ‘yan wasa ‘yan gudun hijira suka fara zuwa gasar Olympic, har zuwa lokacin lashe lambar karramawa da suka samu a gasar a karon karshe, da irin kwazon da suka nuna, wannan rukuni na ‘yan wasa da suka shiga aka dama da su a gasar Olympics ta birnin Paris ta bana, sun yi rawar gani tare da nuna karsashin su na amfani da wasanni wajen sauya yanayin rayuwa.

An dai bude gasar Olympic ta Paris cike da nishadi, an kuma kammala cikin walwala da karfin gwiwa daga bangaren ‘yan wasan tawagar ‘yan gudun hijira, inda a wannan karo suka yi nasarar lashe lambar karramawa ta farko a gasar Olympic.

Wannan tawaga wadda ta fara shiga gasar Olympic a shekarar 2016, yayin gasar da ta gabata a birnin Rio, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta kasa da kasa ko IOC, da asusun ‘yan gudun hijira na gasar Olympic ko ORF, da tallafin hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta MDD UNHCR ne suka kaddamar da ita, da nufin baiwa ‘yan wasan da suka rasa matsugunnan su damar nuna basirar su a gasar kasa da kasa mafi girman matsayi.

Da yake tsokaci game da hakan, mataimakin kwamishina a hukumar lura da ‘yan gudun hijira Kelly T. Clements, wanda ya nazarci tawagar ta ‘yan gudun hijira yayin bikin rufe gasar ta Paris, ya ce "Wadannan ‘yan wasa ‘yan gudun hijira, sun haye tarin kalubale, amma nasarar da suka cimma na tunawa duniya irin abubuwan da za a iya cimmawa, muddin aka baiwa ‘yan gudun hijira taimako har suka kai ga cimma burin su".

A nasa bangare kuwa, shugaban asusun ‘yan gudun hijira na gasar Olympic Jojo Ferris, cewa ya yi "Bayan tawagar ‘yan wasa ‘yan gudun hijira ta kammala gasa mai matukar tarihi, muna iya cewa ‘yan wasan su 37, sun nuna irin nasarar da za a iya samu, idan sun samu cikakkiyar damar gina kan su".

Yayin gasar ta Olympic ta birnin Paris da aka kammala a kwanan nan, ‘yar wasan damben Boxin Cindy Ngamba ta lashe lambar tagulla, a ajin mata masu nauyin kilogiram 75, inda ta zama ‘yar wasan ajin ‘yan gudun ta farko da ta lashe lambar yabo a gasar ta Olympic.

A bangaren ‘yan wasan tsere ajin ‘yan wasa ‘yan gudun hijira kuwa, Dominic Lokinyomo Lobalu, ya kusa lashe lambar karramawa a ajin tseren maza na mita 5,000, inda ya zo matsayi na 4. Kaza lika su ma ‘yan wasan tawagar Perina Lokure Nakang, da Jamal Abdelmaji, sun yi namijin kokari yayin tseren da suka shiga na mita 800 ajin mata, da mita 10,000 ajin maza.

A wasannin cikin ruwa kuwa, tawagogin ‘yan wasa ‘yan gudun hijira ajin gasar tseren kwale-kwale 3, sun kai matsayin wasan kusa da kusan na karshe, inda ‘yan wasa Fernando Dayan, da Jorge Enriquez sun kai ga wannan mataki a tseren kwale-kwale ajin maza na mita 1,000, kana Saeid Fazloula ya kai matsayin a ajin maza na mita 1,000 salon kayak, yayin da Saman Soltani ta kai matsayin a ajin mata na mita 500 salon kayak.

Ko ma dai ina wadannan ‘yan wasa suka kai yayin gasar, ko wane dayan su cikin su 37 din nan ya nuna bajimta da jajircewa, a wasanni daban daban har 12 da suka shiga a gasar ta Paris ta 2024, inda suka daga tutar rukunin al’ummun da aka raba da matsugunnansu, su kimanin miliyan 120 daga sassa daban daban na duniya.

A gasar Olympic ta Tokyo da ta gudana a shekarar 2020 ma, ‘yan wasan ajin na ‘yan gudun hijira su 29 sun fafata a gasar, ciki har da dan wasan tseren kekuna Masomah Ali Zada, wanda ya jagoranci tawagar ‘yan wasa ‘yan gudun hijirar a gasar Olympic ta birnin Paris, a matsayin jagoran tafiyar su, kuma mai magana da yawun su. Yayin bikin bude gasar a Paris, ‘yan wasan taekwondo Ngamba da Yahya Al Ghotany daga tawagar ne suka daga tutar ‘yan wasa ‘yan gudun hijirar.

Har ila yau, yayin bikin rufe gasar ta Paris, ‘yan tawagar Farida Abaroge, da Kasra Mehdipournejad ne suka daga tuta a madadin sauran ‘yan wasan.  Kaza lika, Ngamba, ya hau dandamalin bayar da kyautar karramawa ga ‘yan wasa tare da shugaban IOC Thomas Bach, tare da dan wasan ninkaya daga Faransa Leon Marchand, da sauran wasu ‘yan wasa dake wakiltar nahiyoyi 5 mahalarta gasar, inda suka yi hadin gwiwar kashe wutar gasar ta Olympic, wanda hakan ke alamta kawo karshen gasar.

Kari kan ‘yan wasa da suka shiga aka dama da su a gasar karkashin tutar ‘yan gudun hijira ta IOC, akwai wasu ‘yan wasa maza da mata ‘yan gudun hijira, wadanda a wannan karo suka fito karkashin tutocin wasu kasashe, wadanda su ma suka nuna karsashi, da karfin hali irin na wadanda suka rasa matsugunnan su. ‘Yan wasan sun nuna cewa za su iya kaiwa kololuwar nasara, muddin sun samu dama da tallafin yin hakan.

A wannan rukuni akwai Kimia Alizadeh, wadda a gasar Olympic ta birnin Tokyo ta wakilci ‘yan ci rani, kana a gasar Paris da aka kammala ba da jimawa ba ta wakilci kasar Bulgaria, ta kuma lashewa kasar lambar tagulla ta farko da kasar ta taba samu a wasan taekwondo, ajin mata masu nauyin kilogiram 57.

A daya bangaren kuma, tawagar ‘yan wasan kwallon kwando maza daga Sudan ta kudu, mai kunshe da tsofaffin ‘yan gudun hijira, ciki har da Wenyen Gabriel, wanda ya samu goyon bayan hukumar UNHCR, sun wakilci nahiyar Afirka a gasar Paris, inda suka doke takwararsu ta kasar Puerto Rico, kafin kungiyoyin Serbia da na Amurka su doke su a wasannin rukuni.

Tun dai daga lokacin bikin bude gasar, da dukkanin sassan gudanar da ita, har zuwa lokacin mika kyautukan yabo ga ‘yan wasa da suka yi fice, ‘yan wasa ‘yan gudun hijira sun nuna karfin halin su na cimma nasara, da daga martabar kai, da samar da kwarin gwiwar cimma nasara tsakanin al’ummun da suka rasa matsugunnan su.

Yayin da aka kasha wutar gasar Olympic ta Paris, tarihin da ‘yan wasa ajin ‘yan gudun hijira ya kafa zai ci gaba da karfafa gwiwar kowa da kowa.