logo

HAUSA

Shugaban MDD ya jinjinawa wadanda ta’addanci ya rutsa da su

2024-08-22 13:56:10 CMG Hausa

A jiya Laraba ne sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya jinjinawa wadanda ta’addanci ya rutsa da su, da wadanda suka tsira bayan ta’addanci ya rutsa da su. Yana mai cewa ayyukan ta’addanci na haifar da bakin ciki mara misaltuwa.

Guterres ya bayyana hakan ne a cikin sakon bidiyo a babban taron kasa da kasa, na ranar tunawa da girmama wadanda ta’addanci ya rutsa da su, da ake gudanarwa kowace 21 ga watan Agusta, inda ya ce, "A yau muna tunawa da kuma girmama wadanda ta’addanci ya rutsa da su da wadanda suka tsira." 

Da yake bayyana cewa ayyukan ta'addanci suna haifar da "bakin ciki mara misaltuwa," shugaban na MDD ya ce iyalai da al'ummomin da ayyukan ta'addanci suka wargaza "rayuwarsu ya canza har abada." (Mohammed Yahaya)