logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta cika alkawarinta da ya shafi batun Xizang

2024-08-22 16:19:26 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta jagoranci taron manema labarai a yau Alhamis 22 ga wata, inda aka tambaye ta, mene ne ra’ayin kasar Sin kan ganawar manyan jami’an gwamnatin Amurka da Dalai Lama jiya a New York?

Jami’ar ta bayyana cewa, sanin kowa ne cewa, Dalai Lama na 14, ba malamin addini ba ne zalla, dan neman mafakar siyasa ne dake yunkurin kawo wa kasar Sin baraka, ta hanyar fakewa da batun addini. Kasar Sin tana adawa da duk wata ganawa da jami’an gwamnatocin kasa da kasa suka yi da Dalai Lama, kana tana nuna matukar rashin jin dadinta ga Amurka. Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta fahimci muhimmancin batun Xizang sosai, da cika alkawarin da ta dauka kan batun. (Murtala Zhang)