Wakilin kasar Sin ya bukaci kasashen da abin ya shafa da su gaggauta dage takunkuman da aka kakaba bisa radin kai
2024-08-22 10:42:56 CMG Hausa
Wakilin kasar Sin a jiya Laraba ya bukaci wasu kasashe da su gaggauta janye dukkan takunkuman da suka kakaba bisa radin kai, saboda kakaba takunkumi ba bisa ka’ida ba da wadannan kasashen suka yi, wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, ba kawai kara tabarbare tattalin arziki da zamantakewar kasashen da aka kakaba wa takunkumin suka yi ba, har ma da rura wutar sabon rikici da rashin zaman lafiya.
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya bayyana hakan a gun zaman muhawarar kwamitin sulhu kan batun inganta zaman lafiya da dorewar zaman lafiyan wato sabuwar ajandar samar da zaman lafiya da tattauna batutuwan da suka shafi hana aukuwar rikice-rikicen kasa da kasa da na shiyya-shiyya da na kasa.
Wakilin ya ce, "Hana aukuwar rikice-rikice na bukatar yanayi mai kyau daga waje." Yana mai bayyana rawar da MDD ke takawa wajen hana aukuwar rikice-rikice.
Wakilin ya kuma yi kira ga MDD da ta kara ba da gudummawarta a fannin raya kasa. Yana mai cewa, ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, da ayyukan siyasa na musamman, kamata ya yi su mai da hankali kan bukatun kasashen da abin ya shafa, ta kuma kara yin aiki a bayyane wajen bunkasa tattalin arzikinsu, da ci gaba mai dorewa. (Mohammed Yahaya)