logo

HAUSA

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa sun yi ajalin mutane 114 a Sudan

2024-08-22 11:21:10 CMG Hausa

Jiya Laraba 21 ga wata ne, ma’aikatar lafiya ta kasar Sudan ta sanar da cewa, ruwan sama kamar da bakin kwarya, har da bala’ in ambaliyar ruwa sun afkawa yankuna 47 dake jihohi 10 na kasar, al’amarin da ya yi ajalin mutane 114, kana, adadin mutanen da bala’in ya shafa, ya zarce dubu 110.

Kana, mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa sun tsananta yaduwar cututtuka a kasar ta Sudan, inda ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar da cewa, an samu barkewar cutar kwalara, sakamakon yanayi maras kyau gami da gurbatar ruwan sha.

Sashin hasashen yanayi na kasar Sudan ya ce, za’a kara yin ruwan sama a nan gaba kadan a gabashi gami da arewacin kasar. (Murtala Zhang)