logo

HAUSA

Yamai na karbar bakuncin dandalin Afrika na kula da irin shuka na bana

2024-08-22 11:19:19 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, an bude dandalin Afrika na kula da irin shuka karo na uku, daga ranar 21 zuwa 23 ga watan Augustan shekarar 2024 a birnin Yamai a karkashin kungiyar ’yancin cimaka ta Afrika AFSA, bisa manufar bunkasa da ci gaban irin shuka a kasashen Afrika.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

Kafin kasar Nijar ta karbi bakuncin wannan babbar haduwar kasashen Afrika, dandalin ya gudana a kasar Senegal a shekarar 2022, kana a kasar Tanzaniya a shekarar 2023.

Kasashe 23 suka amsa kiran wannan dandali, daga cikinsu akwai kasar Benin tare da shirinta na JINUKUN, wakilai fiye da dari biyu suke halarta wannan dandali karo na uku da ministan ruwa da muhalli ya jagoranci bikin bude shi a ranar jiya Laraba 21 ga watan Augustan shekarar 2024, a gaban idon sakatare janar na ma’aikatar noma, da daraktar irin shuka, da sakataren musamman kan binciken kimiyya, da darektan dake kula da harkokin kiwo.

Makasudin wannan dandali karo na uku kan kula da irin shuka shi ne jaddada muhimmancin tsare-tsaren irin shuka domin manoma, wajabcin amincewa da irin wadannan irin shuka a hukumance, kare su da samar da moriya ga manoma da kasashen Afrika.

Mamane Ada, sashen Hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.