logo

HAUSA

An samu nasarori da dama kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka

2024-08-22 10:04:24 CMG Hausa

Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labaru a jiya 21 ga wannan wata, inda hadimin ministan cinikayya na kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, bisa jagorancin shugabannin kasashen Sin da Afirka, hukumomi da gwamnatoci da kamfanoni da dama na kasar Sin sun kiyaye yin mu’amala da hadin gwiwa don sa kaimi ga samun nasarori kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka. Kuma nasarorin suna shafar fannoni hudu.

Na farko dai, yawan cinikayyar dake tsakanin Sin da Afirka ya kiyaye samun bunkasuwa. A shekarfar 2023, yawan cinikayyar ya kai dala biliyan 282.1, wanda ya karu da kashi 11 cikin dari bisa na shekarar 2021.

Na biyu, an kiyaye zuba jari da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Ya zuwa karshen shekarar 2023, yawan jarin da kasar Sin ta zuba ga Afirka kai tsaye ya zarce dala biliyan 40, Sin ta kasance daya daga cikin manyan kasashen da suka zuba jari a Afirka.

Na uku, an samu nasarori kan hadin gwiwar ayyukan more rayuwa a tsakanin Sin da Afirka. A cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan kudin kwangilar ayyukan da kamfanonin Sin ta daddale da kasashen Afirka ya zarce dala biliyan 700.

Na hudu, an kara yin hadin gwiwa a sabbin fannoni. Alal misali, a fannin binciken sararin samaniya, kasar Sin ta harba tauraron dan Adam na sadarwa da binciken yanayi ga kasashen Algeria da Habasha da sauransu.

Tang Wenhong ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da daukar sabbin matakan da aka tsara a gun taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka, da kara yin kokari tare da kasashen Afirka don sa kaimi ga bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu mai inganci. (Zainab Zhang)