Kwararru kusan 12,000 ne suka taimaka wajen raya yankin Xizang cikin sama da shekaru 30
2024-08-22 21:06:50 CMG Hausa
Cikin shekaru 30 da suka gabata, kwararru kusan 12,000 cikin kashi 10 ne suka ziyarci yankin Xizang mai cin gashin kansa na kudu maso yammacin kasar Sin, tun bayan fara aiwatar da shirin samarwa yankin taimako daga sauran yankuna.
A shekarar 1994, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta yanke wata muhimmiyar shawara ta samarwa Xizang taimako daga dukkan sassan kasar.
Karkashin shirin, an sanya wasu sassan gwamnatin tsakiya da na matakan larduna da kamfanonin mallakin gwamnati, bayar da taimako ga wasu yankunan na musammam na Xizang, domin karawa aikin raya yankin mai tsaunika kuzari. (Fa’iza Mustapaha)