logo

HAUSA

An yi girgizar kasa a birnin Kuche dake jihar Xinjiang ta kasar Sin

2024-08-22 11:03:35 CMG Hausa

A yau ranar 22 ga wata da karfe 7 da minti 38, an yi girgizar kasa mai karfin maki Ritcher 5 a birnin Kuche dake yankin Aksu na jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Bayar abkuwar girgizar kasar, hukumar ‘yan sanda ta gudanar da aiki cikin gaggawa, da yin bincike a yayin bala’in, har zuwa yanzu, ba a samu hasarar dukiya ko mutuwa da raunatar mutum ko daya ba. (Zainab Zhang)