Sin ta zama zakaran gwajin dafi a fannin goyon bayan zaman lafiya da adalci tsakanin kasashen duniya
2024-08-22 21:18:36 CMG Hausa
Bahaushe kan ce “Zaman lafiya ya fi zama dan sarki”. A duniyar yau mai cike da hargitsi, siyasar nuna karfi, da danniya tsakanin sassan kasa da kasa na ci gaba da haifar da munanan illoli, yayin da tsaron kasa da kasa ke fuskantar mummunan sakamakon hakan.
Sai dai a bangaren ta kasar Sin ta zama zakaran gwajin dafi a fannin sauke nauyin dake wuyanta na tabbatar da adalci, da gaskiya, tare da shiga tsakani wajen warware dukkanin takaddama da kan bullo tsakanin sassan kasashen duniya. Shaidun gani da ido sun tabbatar da dadadden tarihin da kasar Sin ta kafa a fannin aiwatar da matakan diflomasiyya domin wanzar da zaman lumana.
Kama daga gabatar da ka’idojin nan 5 na wanzar da zaman lafiya da lumana sama da shekaru 70 da suka gabata, har zuwa shiga ayyukan gina sabuwar alaka mai inganci tsakanin sassan kasashen duniya, da burin kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil adama a sabon zamani, Sin tana ta daukar matakai na hakika na tallafawa burin wanzar da zaman lafiya da bunkasa ci gaban kowa da kowa.
A fannin gina kyakkyawar alakar kasa da kasa, Sin ta himmatu wajen wanzar da daidato tsakanin kanana da manyan kasashe, inda take mayar da adalci, da kare hakkin ko wane bangare na duniya gaban komai. Don hake ne ma Sin ta kafa tarihin kin goyon bayan mummunar takara tsakanin manyan kasashen duniya, ko goyon bayan siyasar kafa kanan rukunonin adawa da juna. Kaza lika, Sin ba ta shiga siyasar cikin gida ta sauran kasashe, ko matsawa saura domin su goyi bayan wani bangare.
Har ila yau, duk da cewa Sin na fuskantar karuwar matsin lamba, da siyasar nuna karfin tuwo daga wasu sassa, a nata bangare Sin ba ta taba watsi da manufofin ta na kare gaskiya ba. Bugu da kari, Sin na adawa da duk wani yunkuri na wasu kasashe masu fada a ji, dake son yin babakere a harkokin kasa da kasa, tana mai burin ganin dukkanin sassan duniya sun samu tasiri, da bakin fada a ji a harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi, ciki kuwa har da daukacin kasashe masu tasowa.
La’akari da wadannan hujjoji, abu ne a fili cewa Sin ta zama zakaran gwajin dafi, a fannin goyon bayan zaman lafiya, da daidaito da adalci tsakanin kasashen duniya.