logo

HAUSA

An kaddamar da shirin The Bond karo na biyar a kasar Masar

2024-08-21 20:46:10 CMG Hausa

A ranar 20 ga watan Agustan nan ne aka kaddamar da shirin nuna fina-finai shirye-shiryen talabijin mai taken The Bond karo na biyar a birnin Alkahiran Masar a hukumance, wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, da kafofin watsa labarai na Masar, da Kenya da sauran kasashen Afirka suka gudanar tare.

Za a nuna shirye-shiryen talabijin da fina-finai na kasar Sin fiye da 20 cikin harsuna guda 7, kamar Turanci, da Faransanci, da Larabci da sauransu, ta hanyar manyan kafofin watsa labarai sama da 20 na kasashen Afirka 15. A ciki kuma, shirye-shiryen na harsunan Fulfulde, da Amharic za a nuna su a karo na farko ga masu kallo na Afirka. 

Shirye-shiryen gaskiya da na talabijin, da na cartoon da dai sauransu, za su baiwa masu kallon kasashen Afirka damar fahimtar yadda ake gadon kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin a sabon zamani, da ganin saurin bunkasuwar zamantakewar Sin a sabon zamani, da kuma jin dadin kallon fina-finai, da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin da aka maye gurbin muryoyin asali da na ‘yan wasan kwaikwayo da harsunan uwa na gida.(Safiyah Ma)