logo

HAUSA

Ma’aikatar kasuwancin Sin ta soki harajin da EU ta kakaba wa motocin lantarki

2024-08-21 10:13:46 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana a jiya Talata cewa, kasar Sin na adawa da shirin hukumar Tarayyar Turai na sanya harajin kayayyaki da ake shigarwa Turai da ya kai kashi 36.3 cikin dari kan motoci masu aiki da lantarki wato EVs, kuma za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare hakki da muradun kamfanoin kasar Sin.

A watan da ya gabata ne, hukumar ta kakaba karin haraji na wucin gadi da ya kai kashi 37.6 cikin dari kan motoci masu aiki da lantarki kirar kasar Sin, bayan da ta kaddamar da wani binciken kan ba da tallafi ga kamfanonin kera motoci masu aiki da lantarki na kasar Sin a watan Oktoban 2023.

Hukumar a jiya Talata ta wallafa wani daftarin shirin mayar da harajin na dindindin, bayan wani dan kwaskwarima, bisa amincewar kasashe mambobin kungiyar EU.

Kakakin ya ce, wannan tsarin binciken tallafi da hukumar ta yi kan motoci masu aiki da lantarki kirar kasar Sin bai bi ka'idojin kungiyar cinikayya ta duniya ba, kuma wani mataki ne na yin "takara da ba ta dace ba" da sunan "takarar da ta dace". (Yahaya)