logo

HAUSA

Kar Turai ta yi watsi da damar daidaita takaddamarta da Sin kan motoci masu amfani da lantarki

2024-08-21 21:19:30 CMG Hausa

Ranar 20 ga wata, kwamitin kungiyar Tarayyar Turai EU ya kaddamar da bayanan da suka shafi hukuncin karshe da ya yanke kan yin bincike dangane da kin ba da tallafi kan motoci masu amfani da wutar lantarki na kasar Sin, inda ya shawarci a dora haraji na 17% zuwa 36.3% cikin tsawon shekaru 5 kan motocin da Sin da EU suka kera a kasar Sin. Idan za a aiwatar da irin wannan matakin ba da kariyar ciniki a hukumance, za a haifar da babbar illa ga muradun masana’antun motocin kasar Sin, da hadin gwiwar Sin da EU ta fuskar tsarin samar da kaya mai ruwa da tsaki, lamarin da zai yi illa ga ita kanta EU.

Tun daga ranar 21 ga watan Yunin bana har zuwa yanzu, Sin da EU sun yi tattaunawa har sau fiye da 10 dangane da takaddamarsu kan motocin masu amfani da lantarki. Amma EU ba ta tanadi shawarar Sin cikin bayananta ba, ba ta gyara kuskurenta ba. EU ta yanke hukuncin ne bisa gaskiyar da ita kanta ta amince da ita, a maimakon gaskiyar da Sin da EU duka suka amince da ita. Lamarin ya saba wa abun da wasu Turawa suka bayyana, wato mutunta ka’idoji, tafiyar da harkoki bisa doka da yin adalci.

Ainihin hadin kan Sin da EU shi ne neman samun moriyar juna da nasara tare. Har kullum kasar Sin tana nuna sahihanci, tana himmantuwa wajen yin tattaunawa da EU don daidaita takaddamar ciniki. Amma Sin ba za ta kau da kai daga yadda aka illata muradunta ba. Ba za ta sadaukar da muradunta sakamakon matakan ba da kariyar ciniki ba. A ranar 9 ga watan da muke ciki, kasar Sin ta gabatar da kara dangane da matakin EU ga hukumar ciniki ta duniya WTO, matakin da ya nuna cewa, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba domin kiyaye muradun kamfanonin kasarta. (Tasallah Yuan)